Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Mulkin Najeriya bashi da wahala.
Ya bayyana hakane a ganawarsa da gwamnan jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel.
Tsohon shugaban yace tabbas Najeriya kasa ce me girma sosai amma bata da wahalar mulka, gaskiya da Adalci ne zai taimakawa duk wanda ya mulketa.
Ya kuma bayyanawa Gwamnan cewa, neman takarar shugaban kasar da ya fito tana bisa tsari.