fbpx
Monday, June 27
Shadow

Mulkin Nijeriya Na Bukatar Shugaba Mai Dan Tabin Hankali>>Obasanjo

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce Nijeriya na bukatar shugabanni masu ɗan taɓin hankali da za su iya mai da kasar kan turba mai dorewa.

Obasanjo ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban Nijeriya karkashin jam’iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen a Abeokuta, a gidansa da ke Ogun.

Obasanjo yace yana bakin ciki akan halin da Nijeriya ke ciki ba wai kawai koma bayan ba ne gare shi, da kuma wadanda suka damu da Nijeriya baki daya.

Karanta wannan  Hukumar zabe zata karawa 'yan Najeriya lokaci don su cigaba da rigistar katin zabe, cewar Mahmood Yakubu

Tsohon shugaban ya jaddada cewa, Nijeriya za ta iya kawo karshen matsalar tsaron da take fama da ita cikin shekara biyu in ta samu shugaban da ya dace wanda kuma yake fatan daukar matakan da suka dace.

Obasanjo yace yanzu Nijeriya na bukatar shugaba mai dan tabin hakali ne wanda zayyi aikin ba sani ba sabo domin maido da Kasar cikin hayyacin ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.