Thursday, July 18
Shadow

Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 ya soki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan da ta cika shekara guda da kafuwa.

Atiku yace tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ta jefa mafi yawan al’umma cikin halin wahala inda kuma ta talauta masu kudi.

Atiku yace Najeriya bata aiki a karkashin Tinubu inda yace Tinubun ya kasa kawo canji da ci gaban da ya mutane alkawari.

Yace matakan da Tinubu ya dauka sun ma kara jefa mutanene cikin halin kaka nikayi.

Yace matsayin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki a yanzu yafi muni idan aka kwatanta da shekara daya data gabata.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Yace gwamnatin Tinubun ta karawa mutane wahala ne akan wahalar da ake ciki wadda gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta jefa mutane.

Yace Tinubu da mukarrabansa a bayyane take bai san abinda zai yi ba dan dawo da kasarnan kan turba.

Yace lokaci na kara kurewa Gwamnatin Tinubu kuma dolene ya dauki matakan gaggawa dan tseratar da tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *