Kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta NYCN tace itama ba zata bari a cigaba da yiwa wani inyamuri kamfe ba a arewacin kasar nan.
Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan da kungiyar kudancin kasar nan ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa ba zata bari a yiwa dan arewa kamfe ba a Kudu masu gabashin kasar nan.
Inda kungiyar inyamuran tace ba zata bari a yiwa Atiku Abubakar kamfe ba wanda yaci zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP domin zabar shi da akayi kabilanci ne.