fbpx
Friday, May 27
Shadow

Mummunan harin da ‘yan Bindiga suka kai ya lakume rayuka 50 a Zamfara

Ana ci gaba da samun karin haske a kan harin da ‘yan fashin daji suka kai wa Sabon Garin Damri na yankin karamar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Maharan sun halaka mutum kusan hamsin, suka raunata wasu da dama, kuma suka kwashi dukiya mai dimbin yawa, a cewar mazauna garin.

Wani mazaunin garin, Honarabul Mu’azu Damri, ya shaida wa BBC cewa da misalin karfe biyu na rana ne maharan suka auka wa garin.

“Sai muka ji mutane suna gudu suna cewa barayi, barayi, kawai sai muka ji an fara harbi.”

Mahukunta sun ce jami’an tsaro sun kai ɗauki kuma sun samu nasarar kwato kayan da maharan suka diba.

A cewar Honarabul Muazu: “A gaskiya maharan sun yi ta’addanci fiye da yadda ake tunani, sun kwashe dukiyoyin al’umma kuma sun kashe jama’a, sun kashe mutum kusan 48 a kididdigar da muka yi”.

Sai dai ya ce tuni gwamnati ta dauki mataki saboda bayan da aka sanar da mahukunta nan take aka turo da sojoji, kuma sun yi nasarar kwato kayan da maharan suka diba.

Irin wannan hare-hare dai sun zama ruwan-dare a kauyuka da dama na Najeriya, lamarin da ke sanadin rasa dumbin rayuka.

Sai dai mahukunta na cigaba da jaddada cewa suna bakin kokarinsu wajen kawo karshen matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.