Hukumar NDE dake samarwa da ‘yan kasa aiki tace ta baiwa mutanen jihar Akwa-Ibom Miliyan 14.6 a matsayin bashin noma.
Tace mutane 136 ne ta baiwa bashin a cikin watanni 5 da suka gabata.
Daraktan hukumar, Abubakar Fikpo ne ya bayyana haka a Uyo wajan kaddamar da ci gaba da bayar da bashin.
Yace kowane mutum za’a bashi bashin 100,000 akan kudin ruwa kaso 9 cikin 100. Yace kuma ana tsammanin wanda aka baiwa bashin su biyashi cikin shekaru 3.