fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Duk wanda yasan yayi hadari motarsa na tare damu ko wasu kayan Amfani yazo ya dauka nan da kwanaki 14 ko mu sayar dasu>>Yan Sandan jihar Legas

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta gargadi jama’a, musamman wadanda suka yi hatsari da kuma masu motoci ko kayayyakin da aka ajiye su a wasu ofisoshin‘ yan sanda a duk fadin jihar da suje suyi bayani su karbi kayansu ko hukumar ta sayar da su.

Rundunar ‘yan sanda ta tsani yadda ganin motoci da sauran kayayyaki jama’a a cikin ofishoshinsu don haka take umartar Shugabannin rundunoni yan sanda da su ruguza kayan ba tare da bata lokaci ba.

Bisa wannan umarnin, Rundunar Yan sanda ke kira ga jama’a wadanda ke da mota, mashi ko wani da su hanzarta suje suyi bayani su karbo kayansu nan da kwanaki 14, in ba haka ba zasu sayar da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *