fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Mun dai yi iya bakin Kokarin mu amma na yadda cewa ya kamata sojoji su kara kokari>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yadda da shawarar da ake bayarwa cewa sojoji su kara kokari akan wanda suke.

 

Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da gwamnoni a yau inda yace yana samun Rahotanni inda suke bada shawarar ya kamata sojoji su kara akan kokari  da suke kuma shima ya yadda da hakan.

Buhari yace amma mutanen yankin Arewa Maso gabas ya kamata su godewa Sojoji bisa kokarin zaman Lafiya da suke kawowa yankin.

 

Yace gwamnatinsa ta gamu da rashin kayan aiki/ Kudi wanda zuwan Coronavirus/COVID-19 ya taimaka ma hakan sosai.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe sarkin Lafiagi na jihar Kwara

 

Saidai shugaban yace suna iya bakin kokarinsu akan alkawarin da suka daukarwa mutane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.