Harkar bleaching ta zamo ruwan dare yanzu, wanda mata ke amfani da mayukan shafe-shafe domin fatarsu ta kara haske.
Kuma bincike ya nuna cewa a nahiyar Afrika matan Najeriya ne suka fi yin amfani da wa’yan nan mayukan, duk da cewa masani na gargadi akan irin illolin da mayukan ka iya haddasawa masu.
Inda yanzu har ta kaiga wasu daga cikinsu sun fara yin danasanin amfani da wa’yan nan mayukan, kamar yadda wata mata yar jihar Abia ta bayyana mai suna Gold Alfred inda tace man ya kona mata jikinta.