Al’ummar karamar hukumar Birnin Gwari sun yi maraba da shawarar gwamna Matawallen Zamfara inda suka ce sun far kare kawunansu da kansu.
Wani shugaba a masarautar Birnin Gwari kuma tsohon darekta janar na KSMC ne ya bayyaba hakan, watau Alhaji Zubairu Idris Abdulra’uf.
Inda yace tunda gwamnati na gaza kare su zasu fara kare kansu da kansu ko kuma yace sun ma fara domin fusattaun mutanen Randegi sun ci galaba akan ‘yan bindigar da suka kai masu hari.
Saboda haka sun fara kare kansu domin gwamnati ta kasa sauki hakkin kare al’umna daya rataya a wuyanta, kuma manoma sun gaji da biyan miliyoyin haraji ga ‘yan bindigar.