Wednesday, June 3
Shadow

Mun ga wata shi yasa muka yi Idi>>‘Yan Shi’a

Shugaban Mabiya akidar shi’a a jihar Sakkwato Sidi Manniru ya ce sun yi Sallar Idi ne a ranar  Juma’a, 22 ga watan Mayu, domin sun ga watan shawwal bayan sun yi azumin watan Ramadan guda 29.
A zantawarsa da Aminiya, shugaban mabiya Shi’an ya ce tsarin da suka bi na ganin wata shi ne wasu mutane ne da suka yarda da su suka sanar da su an ga watan.
Sanarwar ta ce anga watan ne a garin Dukkuma cikin karamar hukumar Isa da garin Yabo da Illela a sanadin haka babu makawa sai su ajiye Azumi su yi Sallah.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *