fbpx
Monday, August 15
Shadow

“Mun gaji da rokon El Rufa’i ya magance mana matsalar tsaro”>>Kungiyar kudancin Kaduna

Kungiyar al’ummar kudancin jihar Kaduna sun bayyana cewa sun gaji da rokon gwamnan jihar, Malam Nasiru daya magance masu matsalar tsaro a yankunan su.

Inda suka bayyana cewa kashe-kashe ya zamo ruwan dare a kudancin jihar Kaduna kuma kullun cikin bakin ciki suke saboda harin da ‘yan bindiga ke kai masu.

Inda suka ce a ranar biyar ga watan yuni an kai wani mummunan hari a Maikori da kuma wasu kauyuka guda uku a Adara dake Kajuru.

Kuma maharan sun kashe mutane 32 sunyi garkuwa da kimanin mutane 27. Saboda haka su sun gaji da rokon gwamnatin El Eufa’i akan matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published.