Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta gano masu daukar nauyin ta’addanci a Kasar amma ba zata bayyana sunayensu ko kunyata su ba.
Hakan ya fito ne daga bakin ministan shari’a kuma me baiwa shugaban kasa shawara kan shari’a, Mr. Lateef Fagbemi (SAN).
Ya bayyana hakane a Abuja a wajan wani taro kan yaki da satar kudi.
Ya bayyana cewa maganar gaskiya ba zasu bayyana sunayen wanda ke daukar nauyin kashe-kashen ba saboda hakan ka iya kawowa binciken da ake tarnaki.