fbpx
Monday, December 5
Shadow

Mun gano yadda aka kai hari kan ‘yan kungiyar Miyetti Allah da shugabanta – ‘yan sanda

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta ce ta gano yadda aka kai harin da aka kai wa ‘yan kungiyar makiyaya na Miyetti Allah a karamar hukumar Gwagwalada.

Yan sanda sun gudanar da bincike bayan an kashe mambobin kungiyar hudu ciki har da shugabansu a makon jiya.

Rahotanni sun bayyana cewa suna kan hanyar su ne daga kasuwar Izom da ke jihar Neja a lokacin da ‘yan bindigar suka far musu a kusa da kauyen Daku da ke cikin karamar hukumar babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da wasu hudu tare da jikkata da dama da harbin bindiga.

Karanta wannan  Kungiyar Boko Haram ta bayyana cewa itace ta danawa sojojin Najariya bamabamai a Wajiroko da Damboa dake jihar Borno

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, ayyuka, Ben Igwe, ya bayyana cewa “Sun bi su ne suka karbo kudin shanun da suka sayar musu. Muna aiki a kai. Mun gano tushen kuma za mu tabbatar an kama su. Ba na son bayyana abin da muke yi a kan lamarin.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *