fbpx
Monday, August 8
Shadow

Mun kama makiyin Najeriyar daya fitar da jawabin shugaba Buhari tun kamin yayishi>>Femi Adesina

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa sun kama makiyin Najeriya wanda ya fitar da yawabin shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi ta yawo a shafukan sada zumunta, Awanni kadan kamin shugaban yayiwa ‘yan Najeriya jawabin.

 

Jawabin dai ya fita inda aka ga kura kuran rubutu a cikin sa kuma bayan jawabin karshe da shugaba Buhari yayi kan cutar Coronavirus/COVID-19,  an ga cewa jawabin tabbas na shugaban kasar ne, banbanci daya da aka samu shine jawabin da ya fara fita yace ranar 2 ga watan Mayu ne za’a dage dokar hana zirga-zirga yayin da ainahin jawabin shugaban kasar kuma yace Ranar 4 ga watane.

 

Femi Adesina yace tuni har an fara bincikar wanda yayi wannan aika-aika kuma za’a hukuntashi dan wannan cin amanar kasa ne ta hanyar wulakanta ko kuma kunyata fadar shugaban kasa.

 

Ya kara da cewa akwai tsarin da suke bi wajan fitar da sanarwa daga fadar shugaban kasar wanda takardar da aka fitar bata dauke da wannan tsari amma duk da haka sai da aka samu wasu kafafen watsa labarai suka wallafa bayanan dake cikin waccan takarda data riga bayyana kamin jawabin shugaban kasar wanda kuma hakan ya kunyatasu.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ba zata iya aro kudi ta biyawa ASUU bukatunta ba, tace iyaye su roki kungiyar malaman ta janye yajin aiki

 

Yace shine yayiwa jawabin shugaban kasar dubawar karshe kamin shugaban yayi jawabin kuma dan haka da suka ga cewa jawabin ya fita kamin shugaba Buhari yayishi, sai aka rika bin diddigi har aka kai kan wanda ya fitar da jawabin.

 

Yace a rashin sanin wanda ya fitar da jawabin, yanzu zamanin fasaha ne, cikin sauki ake bibiyar mutum a ganoshi idan yayi amfani da yanar gizo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.