Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa Biliyan 2.779 ta kashe wajan yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.
Gwamnatin ta kara da cewa akwai kuma Miliyan 378 da ta samu a matsayin tallafi daga mutane masu zaman kansu da kamfanoni wanda bata kai ga taba su zuwa yanzu.
Gwamnagin ta bayyana hakane daga bakin kwamishinan kudi, Dr. Akinola Ojo wanda yawa manema labarai bayani yau, Talata.
Yace cikin kudin da aka kashe akwai wanda aka saiwa mutane kayan tallafi, da wanda aka kashe wajan tsare iyakokin jihar da wanda aka kashe wajan ma’aikatan Lafiya da dai sauransu.
Yace akwai Miliyan 100 da gwamnatin tarayya tawa jihar Alkawari wanda har yanzu bata cika ba.