Wasu mutane 2 da ake zargi sun amsa laifin kashe wata yar shekaru 38 da take dafawa tsohon dan majalisar jihar Edo Hon. Ezehi MD Igba abinci.
Daga cikin wadanda ake zargin akwai Atiku Yohanna dan asalin jihar Kano, wanda ya kasance yana yiwa Hon. Igbas aiki, sun kai farmaki a gidansa dake Uromi, karamar hukumar Esan Arewa maso Gabas tare da abokinsa a ranar 31 ga watan Maris 2022 da misalin karfe 8 na dare.
Wadanda ake zargin sun shiga dakuna daban-daban suna neman kayayyaki masu daraja.
Mai dafa abinci Mary Atule ta bisu cikin daki inda nan take ta gane Atiku sannan tayi ihun neman agaji, wanda haka yasa suka sassareta da adda har ta mutu.
Lamarin yasa al’umma yankin sun fara zargin Hon. Igbas wanda ya kai ga Yan sanda suka kama shi domin gudanar da bincike.
Yan kwanaki kadan bayan kama Igbas, yan sanda sunyi nasarar cafke wadanda ake zargin a garin Uromi.
Da ake zantawa da su, sun ce sun kashe ta ne bayan ta gane fuskar Atiku.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bello Kontongs, wanda ya tabbatar da kama mutanen biyu, ya ce za a gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar da ko sun aikata irin wannan laifin a wasu sassan jihar Edo.