fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Mun kwashe tsawon Lokaci muna cewa ‘yan Arewa Jahilai amma a yanzu ainahin jahilan suna Fitowa Fili>>Wani Dan Kudu kan hare-haren da ake kaiwa Hausawa

ALLAH SARKI: Yadda Wani Dan Kudu Mai Suna Chigozirim Ya Jajirce Wajen Kare ‘Yan Arewa Da Addinin Musulunci A Kudancin Nijeriya

 

 

Wani dan kudu mai suna Chigozirim Emeakayi ya fatattaki al’ummar kudancin Nijeriya masu cutar da al’ummar Arewa ta hanyar kisa, kone dukiyarsu, da kuma kone wajen kasuwancin su.

 

Chigozirim Emeakayi ya bayyana cewa” ko a lokacin zanga-zangar ENDSARA an kashe al’ummar arewa, an kona dukiyarsu, an kona misu masallatai da wajen kasuwancin su, amman babu wata hukuma ko gwamnatin tarayya wadda ta fito tayi Allah-wadai da wannan aika-aika”.

 

Chigozirim Emeakayi ya kara da cewa “hakazalika, yanzu kuma fada tsakanin fulani makiyaya wanda aka faro a jahar Oyo ya rikide zuwa fada da al’ummar hausawa, ko kuma ince al’ummar musulmi”.

 

Chigozirim Emeakayi ya kara da cewa” Ni abinda ban fahinta ba shine; miye laifin al’ummar hausawa n? Shin idan al’ummar fulani sun mana laifi shi kuma Tumatur da al’ummar da ba fulani ba miye suka mana?”
Chigozirim Emeakayi ya bayyana cewa” wannan fada ba na kabilanci bane, domin al’ummar hausawa basa mayarda martanj, wannan fada ne na ganin bayan Arewacin Najeriya”

 

Hakama, Chigozirim Emeakayi ya bayyana cewa” addinin musulunci addini ne dake son zaman lafiya a duk inda musulmai suke”.

 

Daga karshe Chigozirim Emeakayi ya bayyana cewa” Al’ummar arewa mutane ne kamar kowa, al’ummar arewa ‘yan Najeriya ne kamar kowa, al’ummar arewa sun dade suna hakuri da irin cin zarafin da ake misu, amman a ji tsoron ranar da zasu mayarda martani” a cewar sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *