fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Mun raba tan Dubu 19 na hatsi a jihohin Legas,Ogun, Kano, da Abuja>>Hukumar bada Agaji ta kasa

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa,NEMA ta bayyana cewa ta raba Tan 19,713 a jihohin Ogun, Kano, Legas, da babban birnin tarayya, Abuja dan saukaka matsin da aka shiga kan cutar Coronavirus/COVID-19.

Hakan ya fitone daga jami’in hukumar, Mr. Tope Ajayi, kamar yanda ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN.

 

Yace hatsin da suka raba shine gero, Dawa, da masara.

 

Yace da farko an yi tunanin kaiwa jihohin dake gaba-gaba wajan fama da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ne amma daga baya da cutar ta watsu a Najeriya a yanzu za’a kaiwa jihohu 24.

 

Yace sun hada kai da ma’aikatar jin kai da kula da Ibtila’i dan rarraba wannan hatsi kamar yanda shugaban kasa ya umarta.

 

Yace jihohi na gaba da za’a rabawa wannan hatsi sune, Zamfara Borno da Katsina wanda yanzu haka suna kan aikin rabon.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *