Gwamnatin tarayya ta bayyana samun gibin Naira Tiriliyan 2.23 a watanni 3 da suka gabata na kudin shigarta.
Wannan ya fito ne daga bayanan da aka samu a daga babban bankin Najeriya, CBN.
Bayanan sin bayyana cewa, an samu gibin ne saboda raguwar kudaden siga daga bangaren man fetur da ake sami.
Saidai Rahoton yace ta bangaren kudaden shiga wanda ba na man fetur ba kuma an samu ci gaban samun kudaden shiga.