Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa tayi nasarar kubutar mutane sama da 1000 daga hannun yan bindinga, ba tare da biyan kudin fansa ba.
Matawalle wanda ya fadi hakan yayin wata hira da shi a gidan Talabijin cikin wani shiri mai suna “Sunday Politics”, inda ya bayyana cewa tattaunawarsa da yan bindinga ya taimaka wajen kubutar da mutane da dama.
Ya kara da cewa ya yi imanin idan sauran gwamnoni suka amince da tattaunawa da yan bindinga, ta’addanci zai ragu a Najeriya.