fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Muna bukatar Mutane irin Osinbajo su mulki Najeriya>>Inji IBB

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Wanda aka fi sani da IBB ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar mutane irin su Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo su mulketa.

 

IBB ya bayyana hakane a gidansa dake Naija yayin da wata kungiyar dake goyon bayan Osinbajo ta kai masa ziyara.

 

IBB ya kara da cewa, Osinbajo na da kyakkyawar niyya akan Najeriya. Sannan kuma ya sanshi sosai, mutumin kirki ne.

 

Ya kuma kara da cewa, idan magoya bayan Osinbajon sun je, su gaya masa yana gaisheshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.