fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Muna jiran sunayen ministoci: Majalisar tarayya ta gayawa bangaren zartaswa

Majalisar dattijai a yau, Talata ta bayyanawa fadar shugaban kasa cewa tana jiran jadawalin sunayen mutanen da shugaban kasar ke son baiwa mukaman ministoci a duk sanda aka kammalasu dan su kuma su tantance su.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hakan na cikin Rahoton labaran yau da jaridar The Nation ta wallafa inda aka jiwo cewa majalisar ta kuma ce jiran zuwan sunayen ministocin ba zai hanata tafiya hutun sararawa ba idan lokacin hakan yayi.
A karshen watannan da muke ciki na Yuli ne ake sa ran ‘yan majalisar zasu tafi hutun sararawa.
Shugaban kwamitin dake kula da watsa labarai da hulda da jama’a na majalisar, Sanata Adedayo Adeyeye aya bayyana cewa basu da hurumin da zasu tursasa wa bangaren zartaswa ko kuma tambayar su ko kuma su sau akan shiryawa da mika sunayen Ministocin zuwa ga majalisar, kamar yanda yake a kundin tsarin mulki.
Abinda yake aikinsu kawai shine tantance ministocin bayan shugaban kasa ya gabatar musu dasu, kamar yanda ya fada. Ya kara da cewa dan haka be ga dalilin da zasu damu da aikin da ba nasu ba.
Ya kuma kara da cewa,idan lokacun tafiyarsu hutu yayi, jiran sunayen ministocin bazai hanasu tafiya ba. Dan haka bangaren zartaswa suna da cikakken masaniya akan yanda tsarin majalisar yake sai su yi amfani da lokacin da majalisar kenan kamin ta tafi hutu dan kawo sunayen ministocin.
Yace koda bangaren shari’a a yanzu suna hutu, Alkalan duk sun tafi kasashen waje in banda wanda ke sauraren karar zabe dan haka suma idan lokacinsu yayi zasu tafi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published.