Hukunar Civil Defence ta Najeriya sashen jihar Naija Delta ta bayyana cewa tanada sunayen manyan ‘yan kasar dake da hannu dumu dumu a cikin satar danyen man fetur da rijiyoyi kuma zata bayyana su bada dadewa ba.
Inda ma magana da yawun hukumar Mr. Emeka Peters Okwechime ya bayyanawa manema labarai na Guardian hakanan a Asaba ranar lahadi.
Kuma yace a watan Afrilu na wannan shekarar NUPRC ta bayyana cewa an sacewa Najeriya danyen mai harna dala biliyan 3.6.
Amma yace kokarin da jami’an tsaron keyi yasa ana cigaba da samun ragin barayin danyen man a kasar.