fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Muna nan muma muna shirin yanda zamu bullowa lamarin Arewa, Muna fatan zaku bamu hadin kai>>Ali Jita

Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya bayyana cewa suna nan suma a matsayinsu na sanannu a Arewa suna shirij yanda za’a bullowa lamarin matsalolin Arewa.

 

Yace yasan mutane na maganar cewa a lokacin  da ake yakin neman zaben sun fito sun jawo hankulan mutane, to yanzu ma da ake cikin matsala ya kamata ace sun sake yin magana.

 

Yace indai ‘yan kudu zasu fito cikin kwanaki 3 kacal a kuma biya musu bukatunsu to Arewa ma zamu iya jawo hankalin gwamnati, ta hanyar kiraye-kiraye ko kuma zanga-zangar Lumana.

 

Ali jita ya bayyana cewa ba dan kudi suka yi wannan gwanatin ba. Ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram inda ya kara da cewa akwai inda aka kirasu za’a basu kudi amma dan sunawa wannan gwamnati kyakkyawan zato suka goyi bayanta.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Sakamakon jarabawata ta WAEC ta bata amma tayi matukar kyau don ni ne dalibi na biyu dayafi kokari a shekarar, cewar mataimakin Atiku, Okowa

Leave a Reply

Your email address will not be published.