Abokin takarar Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, Doyin Okupe ya bayyana cewa suna nan suna hada kai da sauran jam’iyyu don kayar da APC da PDP a shekarar 2023.
A yau ranar juma’a Doyin Okupe ya bayyana cewa shine abokin takarar Peter Obi wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar labour Party.
Kuma ya bayyanawa masu labarai cewa suna nan suna hada kai da NNPP, SDP da PRP domin su kayar da manyan jam’iyyun kasar watau APC da PDP