Gwamnatin tarayya ta bakin ministan kwadago, Chris Ngige ta bayyana cewa, tana sane da halin matsin da ‘yan Najariya ke ciki.
Ministan ya bayyana hakane a mahaifarsa dake Alor, Ndemili ta jihar Anambra.
Ya bayyana cewa, dalili ma kenan da yasa ya je mahaifar tasa dan rabawa al’umma kayan masarufi dan samun saukin rayuwa.
Ngige ya kara da cewa, matsin tattalin arziki ba a Najeriya bane kadai, ruwan darene gama Duniya.