Kungiyar masoyan Tinubu da Kashin Shettim ta jihar Legas tace tana yiwa al’ummar Najeriya albishir cewa su zabi Tinubu da Kashim Shettima domin ba zasu taba basu kunya ba.
Inda kungiyar ta kara da cewa zabin da Tinubu yayi na Kashim Shettima ba karamin cancanta yayi ba domin hakan ya karawa jam’iyyar karfin samun nasara a zabe mai zuwa.
A karshe kungiyar Kashim Shettima dan siyasa ne na gari domin yayi aiki tukuru yayin dayake gwamnan jihar Borno kamar yadda Tinubu yayi a jihar Legas.
Soboda haka zasu hada karfi da karfr su maganca matsalolin Najeriya idan suka yi nasarar lashe zabe.