Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa sun ci zamaninsu kuma suna cin na wasu.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumuntar Instagram bayan da ta saka hotonta tare da Rukayya Dawayya.
Wani dai yace musu sun ci zamaninsu gashi suna cin na wasu. Mansurah Isah ta amsa da cewa wannan haka batun yake dan ba’a ce mutum ya kwanta ba.