fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Mune muka cewa Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa, cewar gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa yana daya daga cikin mutanen da suka cewa Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa.

Inda yace kuma hakan ba zai kawo wata matsala a kasar ba domin babbar matsalar itace matsalar tsaro ba banbancen kabilu da addinai ba.

Saboda haka yana kira ga ‘yan Najeriya su marawa APC baya ta cigaba da mulki domin ta cigaba da gyara kasa, kuma maganar Musulmi da Musulmi duk zasu shawo kan matsalar nan gaba.

Karanta wannan  APC ta shigar da karan Tinubu a kotu cewa ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa

Zabar Kashim Shettima da Tinubu yayi ne ya kawo cece kuce a kasar ganin cewa duukansu Musulmai ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.