fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Mune muka kashe dan majalissa da DPO na hukumar ‘yan sanda, cewar ‘yan ta’addan da hukuma ta damke a jihar Bauchi

Hukumar ‘yan sanda ta musamman ta damke wata kungiyar ‘yan ta’adda a jihar Bauchi wadda ta kashe dan majalissa da kuma DPO na hukumar su.

Hukumar Infeto janar ta ‘yan sanda ce tayi nasarar damke su, ‘yan ta’addan sun hada da Hashimu Galadima (Kan Wuka), Abduwahab Abdulhassan (Emeka), Alhaji Hamidu Saleh and Abdulwahab Ahmed (Dan Mama).

Kuma ‘yan ta’addan sun bayyana sunyi garkuwa da mutane marasa adadi yayin da suka kashe wasu al’ummar wanda suma basu san adadin su ba.

Sannan shugabanau Hashim ya bayyana cewa sune suka kashe dan majalissar jihar Hon. Musa Mante saboda baya basu kudi da kuma tsohon DPO na ‘yan sanda saboda ya takura masu kafin yayi ritaya.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.