fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Mune ‘yan majalisar da suke karbar mafi karancin kudi a Duniya>>Sanata Lawal

Kakakin majalisar Dattijai,  Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, Sune ‘yan majalisar da suka fi karbar kudi mafiya karanci a Duniya.

 

Ya bayyana hakane a wani jawabi da ya fitar dan warware rashin fahimtar da ake samu kan yawan Albashin da ake biyansu duk wata.

 

Yace kowane dan majalisar Dattijai na samun Naira Miyan 1.5 kowane wata sai kuma Naira Miyan 1.3 da ake biyan kowane dan majalisar wakilai.

 

Yace Miliyan 13 da a baya aka rika cewa shine Albashinsu ba gaskiya bane, yace ita wannan miyan 13 din ana baiwa kowane dan majalisa ne duk bayan wata 3 dan ya kula da ofishinsa.

Karanta wannan  Kasar Qatar ta sassauta haramcin shan giya saboda gasar cin kofin Duniya

 

Sannan yace su kuma ‘yan majalisar wakilai ana basu Miliyan 8 ne na kula da ofisoshinsu duk bayan wata 3.

 

Idan aka tattara gaba daya kudin,  za’a fahimci cewa, kowane sanata na karbar Naira Miliyan 52 kenan a shekara sannan ‘yan majalisar wakilai na karbar Naira Miliyan 32 na kula a ofis.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

1 Comment

 • KABIRU MUHAMMED BELLO

  Wanan Maganar.
  Tanada Saura
  Saboda Bai yi Cikakenba
  Saboda Akawai Manyan Allowances.
  Da Bai Yi Magana Akansuba.
  Don Haka Maganarsa Bata Nada Gyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.