fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Mune zamu gyara Najeriya a 2023>>PDP

Shugabannin babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya wato PDP ta yi alwashin kwace Mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekara ta 2023.

Shugabannin PDP sun wannan ikirarin ne a wajen rantsar da sabbin ƴan kwamitin gudanarwar jam’iyyar a Abuja, suna zargin APC da gazawa wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya, don haka ya kamata a yi waje da ita.

Babban lauyan jam’iyyar PDP kenan, yana jagorantar sabbin shugabanni ko ƴan kwamitin gudanarwar jam’iyyar wajen shan rantsuwar kama aiki.

Mafi yawan masu jawabi a wajen bikin rantsuwar, ciki har sabon shugaban jam’iyyar, Senata Iyrochia Ayu sun caccaki jam’iyyar APC mai mulkin Najeriyar suna cewa ta gaza wajen cika alkawuran da ta yi na kyautata rayuwar ƴan kasar.

Iyorchia Ayu ya yi zargin cewa tattalin arzikin Najeriya ya durkushe, tsaro ya tabarbare har an shuga yanayin da iko da wasu sassan kasar ya koma hannun ƴan ta’adda.

Kana ya yi alwashin cewa idan PDP ta karbi Mulkin Najeriya komai zai daidaita.

Sai dai jam’iyyar APC ta sha musanta zargin da ake mata na gazawa, tana ikirarin cewa tana bakin kokarinta, kuma jam’iyyar PDP babatu kawai take yi, irin wanda ƴan magana kan ce na zaune gwanin kokawa.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ta sha Alwashin magance matsalar yin kashi a waje

Sabbin shugabannin PDPn dai sun karbi jagorancin jam’iyyar ne a daidai lokacin da rikicin cikin gidan ya dabaibaye jam’iyyar, musamman ma zargin da ake yi cewa gwamnoni sun kwace iko da jam’iyyar, don haka sabbin shugabannin ma watakila su kare a ƴan amshin shata.

Amma sabon mataimakin shugaban jam’iyyar PDPn na yankin arewacin Najeriya, Ambasada Umar Iliya Damagun ya ce da ganin linzami ya fi bakin kaza! Don haka sun wuce zama karan kada miyar wasu.

Wasu daga cikin ƴaƴan jam`iyyar sun bayyana fatan da suke yi wa sabbin shugabannin.

Senata Iyorchai Ayu dai shi ne shugaban jam`iyyar PDP na kasa na goma sha shida, idan aka hada lissafi da mutum biyar da suka riki mukamin a matsayin riko.

Kuma baki dayan wadanda suka hau kujerar ta hanyar zabe, babu mutum guda da ya kammala wa’adin mulkinsa lafiya-lafiya sakamakon rikicin cikin gida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.