fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Musulmai na sallah a tsakiyar titi a kasar faransa saboda karancin masallatai

Masallata a kasar Faransa na salla a kan tituna
Musulmai a kasar Faransa sun koma yin sallah a tsakiyar tituna saboda karancin masallatai a kasar, Lamarin baya-bayannan daya faru shine wanda ya farane a watan Maris da ya gabata bayan da wani sabon maganjin gari ya rufe wani masallaci(Babban dakine da musulami suka amsa haya suke sallah a ciki) ya mayar dashi dakin nazari/karatu, sai ya ba musulman wani sabon guri can gefen gari yace su rinka sallar acan, su kuma sukace gurin ya musu nisa kuma bazai dauke yawansu ba, dan haka sai musulman a wani yanayi na nuna adawa da wannan mataki suka fara yin sallar a kan titi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Tun daga lokacinne musulmai da yawa kawai suke haduwa suna salla a kan tituna tunda dama koda can ma babu isassun masallatai a kasar.

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa
Magajin garin da wasu ‘yan siyasa sun fito yin zanga-zangar nuna adawa da sallar da musulman keyi akan titi, ranar 10 ga watannan na Nuwamba da muke ciki, kamar yanda kafafen watsa labarai na RT da Independent ta kasar Ingila suka ruwaito.
 Masallata na salla a tsakiyar titi a kasar Faransa_Reuter
Amma ‘yan sanda suka taresu saida musulman suka kammala sallah. Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransar dai ya bayyana cewa za’a magance matsalar yin sallar musulman a kan titi kuma za’a samarwa musulman gurin yin sallah daya dace.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

RT/Independent.uk

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *