fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Musulman jihar Osun sun fito zanga-zanga, sunyi Allah wadai da malaman dake kashe mutane domin sadaukar dasu

Musulman dake Iwo a jihar Osun sunyi zanga-zangar limana akan masu kashe mutane da manufar sadaukarwa inda sukace ya kamata gwamnati ta riga hukunta su.

Sun gudanar da zanga-zanfar ne a tsakiyar garin Iwo inda sukace inda suka rike wasu fastoci dauke da taken “Malamai basa kashe mutane da manufar sadaukarwa.”

A cikin mutanen hadda kungiyoyin Musulmai kamar su Ansarul-Huda wanda shugabansu Shafi’i Bello yace Musulunci ya hana kashe mutane da kuma saida wani bangare na jikin su, kuma musulmi na gari ba zai aikata wannan ba.

Yayin da shima shugaban kungiyar NASFAT Sheik Tajudeen Bilal yace wannan babban laifi ne wanda duk Musulmi na gari ba zai aikata ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.