A yau Litinin 25/4/2022 a zaman tafsirin Maulana Khalifa Malam Abdulganiyyu, wanda aka saba gabatarwa a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano bakin kasuwar Getso kofar gidan Alh Sule zama na 26 musulumci ya samu karuwa, inda muka karbi wani bawan Allah dan Kwanar Dangwauro mai suna David a baya wanda yanzu ya zabi da a mayar masa da sunansa Mvuhammadu.


Daga Mukhtar Lawan Liver Gwarzo