Rahotannin da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana na jiya, Talata sun tabbatar da cewa mutane 10 ne suka mutu cikin awanni 24 da suka gabata sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19.
Sannan rahoton ya bayyana jihar Filato a matsayin jiha mafi yawan masu kamuwa da cutar. Daga cikin jimullar mutane 239 da suka kamu da cutar a jiya, 116 daga jihar Filato suka fito.
Wannan dalili yasa hankula suka koma kan jihar ta Filato. NCDC ta kuma tabbatar da mutuwar mutane 10.