An samu labari mutane 12 sun mutu bayan da ‘yan vigilanti da ‘yan bindiga sukayi musayar wuta a tsakaninsu a jihar Filato.
‘Yan bindiga tara ne suka mutu sai ‘yan vigilanti guda uku a musayar wutar da sukayi a karamar hukumar Zak ranar lahadi.
Mai magana da yawun hukumar hadakar jami’ai ta OPSH, Mejo Ishaku Takwa ne ya bayyana hakan amma bai fafi adadin mutanen da suka mutu ba.
Kuma yace rundunar soji ta kawo masu agaji a farmakin da ‘yan bindigar suka kawo mata.