A kalla Mutane 13 ne a ranar Litinin da yammaci suka tsallake rijiya da baya a wani hadari da ya faru a jihar Anambra.
Da take tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Florence Edor, ta ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 1:40 na dare a yankin Upper Iweka da ke cikin garin.
Hatsarin ya rutsa da wani direban motar Toyota Harrier Jeep mai lamba AAA 935 FN, da wani direban da ba a bayyana ko wanene ba a wata motar bas.
A cewar Jami’in jimillan mutane goma sha bakwai ne suka yi hatsarin wanda ya kunshi maza manya da mata manya bakwai da yaro daya.
Hakanan suma Wasu shaidun gani da Ido sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka bayyana cewa lamarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa’a.
Sai dai ba’asamu a sarar rayuka ba.