fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Mutane 14 ake kashewa a kullun a Arewacin Najeriya

Kungiyar masu kafafen yada labarai na Arewacin Najeriya, (NBMOA) ta bayyana cewa, a kullun akwai mutane 14 da akw kashewa a Arewa.

 

Kungiyar tace a shekarar 2021, mutane 8,372 ne aka kashe a Najeriya.

 

Shugaban riko na kungiyar, Abdullahi Yelwa ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.

 

Yace akwai yara Miliyan 10.5 da basa zuwa makaranta sannan akwai ‘yan gudun hijira miliyan 2.7 da suka rasa mahallansu.

 

Yace duk masu neman takarar shugabancin Najeriya, ya kamata su fito da tsari ta yanda zasu magance wadannan matsalolin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *