fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Mutane 15 da aka yi garkuwa dasu sun tsere yayin da wanda suka yi garkuwan dasu suka yi tatul da giya a Zamfara

Mutane 15 da aka yi garkuwa dasu a Tegina jihar Naija, aka kaisu jihar Zamfara, sun tsere daga hannun wanda suka yi garkuwa dasu din yayin da suka yi tatul da giya.

 

Mutanen na tare da daliban Islamiya da aka sace a makon da ya gabata, amma daga baya sai aka rabasu, aka kaisu Zamfara.

 

A daren ranar Juma’a ne dai wanda aka sace din suka bude dakin da aka ajiyesu a ciki suka sulale yayin da wanda ke gadinsu suke bacci bayan sun sha giya.

Karanta wannan  Sanata Ndume yace rayuwa a Maiduguri tafi kwanciyar hankali akan Abuja saboda matsalar tsaro

 

Bayan fitowarsu daga gidan, Punchng ta ruwaito cewa, sun raba kansu kowa ya kama hanyarsa dan kada su tafi a hade a ganesu, wasu daga cinkinsu, sun tsinci kansu a Zaria inda sojoji suka taimaka musu.

 

Daya daga cikin wanda suka tsero ne ya bayyana yanda lamarin ya kasance bayan da ya koma gida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.