Sakamakon gwajin da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, Jiya Laraba na nuni da cewa mutane 15 ne suka mutu a Najeriya a rana 1.
An samu karuwar masu cutar har guda 460 wanda ya kawo jimullar wanda suka kamu da cutar zuwa 30, 249.
Mutane 15 ne suka mutu a rana 1 wanda ya kawo jimullar wanda suka mutu zuwa 684. Jimullar wanda suka warke kuma sune 12,373.