fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Mutane 18 ne suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Katsina

Akalla mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu mutane shida suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kife a cikin wani kogi da ke karamar hukumar Mai’adua ta jihar Katsina.

A cewar wani mazaunin garin, Lawal Sakatare, kwalekwalen da ke dauke da masu shagulgulan Sallah 24 ya kife da misalin karfe 11:00 na daren ranar Laraba, 4 ga watan Mayu. Galibin wadanda suka nutse kananan yara ne.

Ya kara da cewa, tawagar da ta fito daga kauyukan da lamarin ya shafa na ci gaba da aikin ceto sauran shidan, duk da cewa fatan samun su da rai ya dushe.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo na daga cikin manyan baki da suka halarci jana’izar wadanda suka mutu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *