fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mutane 2 sun mutu, an harbi dan sanda a fashin hanyar Kogi

Lamarin ya farune da misalin karfe 6 na yammacin jiya, Lahadi a daidai Osara, tsakanin Itakpa da Kabba inda ‘yan fashi suka bude wuta.

 

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Fashin sun kashe mutum 2 tare kuma da harbin wasu ciki hadda dan sanda.

Wanda suka mutu din ‘yan asalin Kogi ne dake zaune a jihar Katsina, kuma sun dawo daga ganin gidane yayin da lamarin ya faru.

 

Wata mata data tsallake harin ta shaidawa Punch cewa, harin ya saka fargaba azukatan mutane kuma da dama sun shiga halin kaka nikayi inda aka tara motoci da yawa akan hanya.

Karanta wannan  Mutane 12 sun mutu a musayar wutar da 'yan bindiga suka yi da vigilanti a jihar Filato

 

Saidai ‘yansandan jihar sunce basu da masaniya akan wannan hari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.