Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa, a jiya, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, mai shekaru 64 da kuma wani jariri, sakamakon hatsarin mota wanda ya faru a karamar hukumar Gumel.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Zubairu Aminudeen, a cikin wata sanarwa, ya ce wasu mutum shida sun samu raunuka a cikin hatsarin.
DSP Aminudeen ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Gumel zuwa Hadejia da ke Gumel da misalin karfe 9 na safe lokacin da direban wata mota kirar Toyota Sharon “ ta kuce mashi sannan motar ta wuntsila ta fada cikin rami. Sakamakon haka, wani Usman Mohammed (64) daga Karamar Hukumar Nguru na Jihar Yobe da wani Hamza Mohammed (watanni 7) suka mutu.