Kimanin matafiya 20 ne suka kone kurmus a wani hatsari da ya rutsa da motocin kasuwanci guda biyu a kauyen Huturu, dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano a jiya.
Hadarin dai ya hada da wata mota kirar Golf Volkswagen, wadda ta yi karo da wata karamar bas ta Sharon dake jigilar fasinjoji da kayayyaki.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Yusuf Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa mutane 21 ne a cikin motocin kasuwanci guda biyu, ya kara da cewa daya daga cikin direbobin ya tsira.
Ya kara da cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon mugun gudu. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Talata. Jami’an su sun samu rahoton ne da misalin karfe 11:38 na safe kuma mun isa wurin da misalin karfe 11:50 na safe. Wani direba ya ji rauni, wasu 20 kuma sun kone kurmus,” inji shi.
Allah ya musu rahama Allah yasa sun huta