Lamarin ya farune a kogin Shagari dake karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.
Rahotanni sunce ana kan binciken gawarwakin wanda suka nutse.
Shugaban karamar hukumar Shagari, Aliyu Dantani ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN haka a ganawarsu a Sokoto.
Yace 21 daga cikin wanda aka ceto matane sai kuma 5 yara inda yace ana ci gaba da aikin ceton.
Ya kara da cewa, zuwa yanzu ba’a san mutane nawane a cikin jirgin ruwan ba.