fbpx
Monday, June 27
Shadow

Mutane 200 sun rasa muhallansu dalilin ambaliyar ruwa a jihar Jigawa

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa, SEMA ta bayyana cewa, mutane 200 ne suka rasa muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwa.

 

Sakataren hukumar, Alhaji Yysuf Sani Babura ne ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Yace kananan hukumomi 10 ne ambaliyar ruwan ta shafa a shekarar data gabata.

Ya bayyana Gwaram, Garki, Babura, Jahun, Miga, Kaugama, Giuri, Maigatari, Birniwa da Birni Kudu, a matsayin kananan hukumomin da abin ya shafa.

 

Ya bayyana cewa an zabi mutane 100 daga cikin wanda ambaliyar ruwa ta shafa aka tallafa musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.