Hukumar kiyaye haddura ta kasa, a ranar Alhamis, ta tabbatar da mutuwar mutane 21, ciki har da yara ‘yan makaranta, a wani hatsarin mota a Mgbowo da ke karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.
Kwamandan sashen na Enugu, Mista Ogbonna Kalu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The PUNCH, ta wayar tarho, ya ce hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Laraba.
Ya ce hatsarin ya rutsa da motar makaranta da tirela.
Kwamandan ya dora alhakin hatsarin kan saurin wuce gona da iri da tuki mai hatsari.
Kalu ya ce, “An tabbatar da mutuwar mutane 21 kuma sama da mutane 50 na cikin motar makarantar.
“Har ila yau, abin lura shi ne, ba duk wanda suka mutu a motar yan makarantar ba ne. Wadanda ke aiki a gefen hanya na daga cikin wadanda suka mutu.
“Daga bayanan da ke akwai, hatsarin ya faru ne sanadiyyar tuki mai hatsari.”
Jaridar Punch, ta tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar mota kirar Lowbed mallakar wani kamfanin gine-gine da ke aiki a kan titin Oji-River-Awgu ta kucci ma matukin kuma ta fadawa motar bas din da ke dauke da dalibai sama da 60 na yan makaranrar firemare mai suna Presentation Nursery, Awgu. mallakar Katolika Diocese na gidan Awgu.