fbpx
Monday, August 8
Shadow

Mutane 3 dake da Coronavirus/COVID-19 a Kano sun tsere daga inda ake killace dasu sun kuma kashe wayoyinsu

Rahitanni daga jihar Kano na cewa wasu mutane 3 daga cikin wanda ake killace dasu a jihar masu dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 sun tsere daga inda ake killace dasu din.

 

Me kula da tsare-tsaren kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar, Tijjani Husainine ya shida haka.

 

Ya kuma bayyana cewa sun je gidajen wadannan mutane amma basu tarar dasu ba.

 

Yace dan haka sun nemi taimakon jamian tsaro dan nemo mutanen a mayar dasu wajan killacewar. Yace saidai abin farin ciki shine makwautan mutanen sun san halin da ake ciki.

 

Ya gayawa Premium times cewa a yanzu mutane 73 ke killace a gurin killace masu cutar na Kano.

 

An dai samu jimullar mutane 77 dake dauke da cutar a jihar amma an samu tangarda inda aka tsayar da gwajin cutar saboda rashin isassun kayan aiki.

 

Attajirin dan kasuwa daga Kanon, me kamfanin BUA,Abdulsamad Rabiu a jiyane ya sake bayar da Naira Biliyan 3.3 na tallafin Coronavirus/COVID-19 bayan tallafin daya bayar a baya na Naira Biliyan 1.6

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.